Gwamnatin Tarayya ta ce shirye-shiryenta na koyar da sana’o’i da ƙarfafa matasa an tsara su ne domin dakile talauci.
Gwamnatin Tinubu ta shirya fitar da matasan Najeriya miliyan biyar daga talauci da kuma samar da hanyoyin samun abin dogaro mai ɗorewa.
Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Ilimin Fasaha, Sana’o’i da Kasuwanci, Dr Abiola Arogundade, wadda ke jagorantar shirin, ce ta bayyana hakan yayin fara matakin shirin a Jihar Oyo, wanda zai gudana daga ranar 28 ga Satumba zuwa 9 ga Oktoba.
Ta ce shirin ya fara ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja, kafin a kai shi Jihar Oyo, kuma daga bisani za a faɗaɗa shi zuwa sauran jihohi da yankunan siyasar ƙasar.
