Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta wani rahoto da ya ce gwamnatinsa ta yi tayin sassauta wasu takunkuman da aka kakaba wa Iran.
Batun na zuwa ne yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da tattaunawa ta hannun masu shiga tsakani kan yakin da kuma batun makaman nukiliyar Iran.
Iran na neman a sassauta takunkumi tare da sake buɗe mashigin Hormuz, yayin da Amurka ke neman a samu ci gaba kan batun nukiliyar ƙasar.
Ana ci gaba da sa ido kan matakin da bangarorin biyu za su ɗauka yayin da ake ƙoƙarin samun hanyar diflomasiyya
