An gano gawarwakin mutane huɗu bayan kifewar wani jirgin ruwa ɗauke da masu yunƙurin ƙaura zuwa Turai a gabar tekun Senegal, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka ɓace.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, 18 ga Nuwamba, a kusa da garin Yenne da ke kudancin Dakar, babban birnin ƙasar.
Wani jami’in yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa jirgin na ɗauke da aƙalla mutane 50, kuma ya bugi dutse yayin da ake ƙoƙarin kwashe fasinjoji daga ƙananan jiragen kamun kifi zuwa wani babban jirgin katako.
Shugaban ƙungiyar agaji ta Horizons Sans Frontières, Boubacar Séye, ya tabbatar da gano gawarwakin huɗu, sai dai har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka ɓace ba.
Hatsarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar masu yunƙurin tsallaka tekun Atlantika daga yammacin Afirka zuwa tsibiran Canary na ƙasar Spain.
Rundunar sojin ruwan Senegal ta bayyana cewa ta ceto ko tare sama da mutane 1,400 da ke yunƙurin zuwa Turai cikin sa’o’i 48 a wannan makon.
A nasa ɓangaren, Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen daƙile ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, tare da samar da ƙarin damar ayyukan yi ga matasa.
