24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiAn Cire sunan Osimhen Daga Jerin Ƴan Wasan Najeriya 

An Cire sunan Osimhen Daga Jerin Ƴan Wasan Najeriya 

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

An cire dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Napoli, Victor Osimhen a cikin jerin ‘yan wasan da za su buga wasan sada zumunta na kasa da kasa tsakanin Super Eagles ta Najeriya da kasar Aljeriya.

 

An tilastawa Osimhen ficewa daga jerin Ƴan wasan ne sakamakon rauni daya samu a wasan da Napoli ta doke Liverpool da ci 4-1 a daren Larabar makon jiya.

 

A yau ranar Asabar ne Babban kocin Super Eagles, José Santos Peseiro, ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasan da aka gayyata a wasan da za a yi ranar Talata, 27 ga Satumba.

 

Daga cikin jerin sunayen akwai kyaftin Ahmed Musa, mataimakin kyaftin William Ekong. Sauran Ƴan wasan da zasu taka ledar sun hada da; Francis Uzoho, Maduka Okoye, Kenneth Omeruo, Chidozie Awaziem, Calvin Bassey,  Wilfred Ndidi da kuma Alex Iwobi.

Latest stories