Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniWasan hamayya tsakanin Real Madrid da kuma Atletico Madrid

Wasan hamayya tsakanin Real Madrid da kuma Atletico Madrid

Date:

Daga Ahmad Hamisu Gwale.

 

A wannan rana ra Lahadi ne za’a buga wasan hamayya tsakanin kungiyoyi biyu da suke a birni daya, wato Real Madrid da kuma Atletico Madrid.

 

Wasan dai zai gudana a filin Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid a kasar Spain, kuma wasan zai zama zakaran gwajin dafi tsakanin manyan kungiyoyin da suke birnin na Madrid.

 

Tuni dai aka jiwo dan wasan bayan Real Madrid wanda ta dauka daga Bayern Munich David Alaba ya bayyana wasan dana musamman.

 

Harma ya bayyana kungiyarsa ta Madrid din ka iya nasara a kan Atletico Madrid da kaso 100.

 

A kakar wasannin da ta gabata dai, Madrid itace ta lashe gasar ta La Liga, wadda kuma a yanzu ta ke kokarin ganin ta kare kan bumta.

 

A gefe guda abokiyar hamayyar Real Madrid tuni ta koma matakin farko a ranar Asabar, bayan dan wasa Robert Lewandowski ya zura kwallo biyu a wasan da Barcelona do ke Elche da ci uku da nema.

 

Kawo yanzu dan Kasar Poland lewandowski ya zura kwallo 11 a Barcelona a duka wasa takwas da fara sabuwar kakar wasanni ta bana.

 

Sai dai kungiyar ta Barcelona ta buga wasa shida ne, wanda hakan ya bata damar kasancewa a matakin farko da maki 16.

 

Sai kuma Real Madrid na mataki na biyu a teburin gasar ta La Liga da maki 15 bayan buga wasa biyar, wanda idan tayi nasara akan Atletico Madrid to zata koma matakin farkon da take.

 

Ita kuwa Athletico Madrid tana mataki na 7 da maki 10 bayan buga wasa biyar jumullla a kakar wasannin ta bana.

 

Amma Real Madrid zata buga wasan na hamayya ne batare da dan wasan gabanta Karim Benzema ba, sakamakon raunin da yaji a baya.

 

Wanda hakan ya sanya dan wasan kasar Brazil Vinicius JR shi ne zai jagoranci ‘yan wasan da zasu ziyarci katafaren filin wasa na Wanda Metropolitano domin buga wasan a wannan rana ta Asabar 18 ga Satumbar 2023.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories