Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Thursday, April 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniZan iya lashe kyautar Ballon d’Or a Barcelona –Lewandowski

Zan iya lashe kyautar Ballon d’Or a Barcelona –Lewandowski

Date:

Dan wasan Barcelona Robert Lewandowski, ya bayyana cewa zai iya lashe kyautar Ballon d’Or.

 

Lewandowski wanda ya koma Barcelona daga Bayern Munich a kan kudi fam miliyan £50 a kakar wasannin da muke ciki.

 

Dan kasar Poland ya fafata kakar wasanni takwas a tsohowar kungiyarsa da ke Allianz Arena, ya zura kwallo 344 a wasanni 374 da ya buga mata a baya.

 

Haka kuma a yanzu a Barcelona Lewandowski ya zura kwallo 11 a wasa takwas a kakar wasanni ta bana.

 

Wanda hakan ya bashi damar kasance a gaba a yawan zura kwallo a gasar La Liga a gaban dan wasa Karim Benzema da kuma Iago Aspas.

 

Mai shekara 33 tuni yayi hasashen cewa shi ne zai lashe kyautar ta Ballon d’Or a kungiyarsa ta Barcelona.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...