Jam’iyyar ADC ta haramta wa dukkan rassanta na jihohi karɓar takardun shari’a ko ɗaukar lauyoyi su wakilci jam’iyyar ba tare da sahalewar hedikwatarta ta ƙasa ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, inda ya bayyana cewa daga yanzu duk wata takardar shari’a da aka miƙa wa rassan jihohi dole ne a tura ta kai tsaye zuwa Ofishin Mai Ba Jam’iyyar Shawara Kan Harkokin Shari’a na Ƙasa da ke Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bai wa wannan ofishi kaɗai ikon naɗa lauyoyi ko wakiltar jam’iyyar a gaban kotu.
Jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa duk wani reshe ko jami’i da ya karya wannan umarni ta hanyar ɗaukar lauya ko gudanar da harkokin shari’a ba tare da izini ba, zai fuskanci matakan ladabtarwa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.
