Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya ce lauyoyi na da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da bin doka da oda, tare da kare martabar tsarin damukradiyyar Najeriya ta hanyar ganin an gudanar da zaɓen shekarar 2027 mai tunkarowa cikin lumana, adalci, gaskiya da sahihanci.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron shekara-shekara karo na biyu da kungiyar matasan lauyoyin arewacin Najeriya suka gudanar a Kano.
Gwamna Abba ya buƙaci matasan lauyoyin su kasance masu riƙon amana, ƙwarewa da gaskiya a aikinsu, kuma su guji cin hanci da rashawa, tare da sadaukar da kansu wajen yiwa al’umma hidima, tare da yin kira ga manyan lauyoyi da alƙalai da su farfaɗo da al’adar baiwa matasan laiyoyi shawarwari, domin taimaka musu su zama ƙwararru kuma masu nagarta.
A nasa jawabin, Babban Lauyan gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Abdulkarim Kabir Maude SAN, ya buƙaci matasan lauyoyin da su kasance masu ɗa’a, ƙwarewa da kishirwar tabbatar da adalci.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, Barrister SAN ya kuma ƙarfafawa matasan lauyoyin gwiwa kan su ci gaba da neman ilimi, su kare bin doka da oda, tare da amfani da iliminsu wajen inganta shugabanci nagari da ci gaban ƙasa.
