Saurari premier Radio
24.2 C
Kano
Monday, September 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniAbin da ya sa nayi murabus daga kwallon kafa –Mikel Obi

Abin da ya sa nayi murabus daga kwallon kafa –Mikel Obi

Date:

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles John Obi Mikel, ya sanar da yin murabus daga fagen kwallon kafa.

 

Mikel Obi dai ya sanar da yin murabus ne bayan shafe shekaru 20 ana fafatawa da shi a fagen kwallon kafa.

 

Kuma dan wasan ya yi murabus ne yana da shekara 35, wanda ya lashe gasa daban-daban a duniya kama daga kasa da kuma kungiyoyin da ya wakilta, cikin gasannin da ya lashe har da Nations Cup, da kuma Champions League.

 

Da kansa dan wasan ya sanar yayi murabus a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a wannan rana ta Talata.

 

“Matuka kowa ya san da cewa duk abin da yayi farko to shakka babu yana da karshe, kuma a wannan rana nake mai cewa na kawo karshen buga wasa a fagen tamaula’’

 

“Akalla na shafe shekaru 20 ina buga kwallo, kuma nida kaina na gamsu cewa na gamsu lokaci yayi da zan koma gefe domin zama dan kallo’’ a cewar Obi.

 

Dan wasan ya kuma kara da cewa matuka babu wani abu da zai kasance ka samu goyan baya musamman a fagen kwallon kafa, muddin baka samu goyan bayan iyalai manajoji, abokan wasa, masu horarwa dama uwa uba magoya baya a fadin duniya.

 

Mikel Obi dai ya fara buga wasa na farko a tarihin rayuwarsa a kungiyar kwallon kafa ta Plateau United a shekarar 2002 zuwa 2004.

 

Kafin kuma ya koma kungiyar kasar Norwegian wato Lyn Oslo a shekarar 2004 a lokacin ya na dan shekara 17, kuma ya buga wasa 6 da zura kwallo daya.

 

Sai kuma ya koma Chelsea ya shafe lokaci wato daga 2006 zuwa 2017, wanda kuma ya buga mata wasa 246 da zura kwallo 1 kacal.

 

Haka kuma ya buga kungiyoyi irinsu Tianjin TEDA da Middlesbrough da Trabzonspor da kuma Stoke City.

 

Inda kuma ya buga kungiyar karshe wato SC Kuwait a shekarar 2021.

 

A tawagar Super Eagels kuwa ya buga wasa 91 da nasarar zura kwallo 6 tin daga shekarar 2006 zuwa 2019 da ya sanar da daina wakiltar Najeriya.

 

Ya kuma lashe gasar Premier League da gasar FA Cup da Football League Cup da FA Community Shield da UEFA Champions League da kuma UEFA Europa League.

 

A tawagar Super Eagles kuwa ya lashe gasar cin kofin nahiyar afrika ta AFCON a shekarar 2013

Latest stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Sabbin Yan Wasa 12 da Kano Pillars ta dauka

Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars, wadda ta lashe...