Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniIbrahim Musa Gusau ya zama sabon shugaban NFF

Ibrahim Musa Gusau ya zama sabon shugaban NFF

Date:

Alhaji Ibrahim Musa Gusau, ya zama sabon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta kasa NFF bayan zabe karo  40

 

Ibrahim Gusau dai shi ne shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Zamfara, wanda aka gudanar a ranar Jumma’a 30 ga Satumba 2022, a jihar Edo.

 

Ya yin kaɗa ƙuri’ar da akayi a zaben Gusau, ya samu kuri’u 21, sai kuma Seyi Akinwumi ya zo na biyu da kuri’u 12 inda kuma Shehu Dikko da ya zo na uku da ƙuri’a 7.

 

Haka zalika Abba Yola da Peterside Idah sun zo na hudu dana biyar da yawan kuri’u 1.

 

Tuni dai bayan kammala kada kuri’un, jagororin gudanar da zaben sun tabbatar dacewa zaben bai kammala ba.

 

Inda aka bayyana sai an sake zuwa zagaye na biyu , da hakan ta sa ‘dukkanin ‘yan takara suka janye daga zaben banda Peterside Idah.

 

A zagaye na biyu na kada kuri’un, Ibrahim Musa Gusau, ya samu ƙarin kuri’u 9, ya yinda abokin karawar sa Idah bai samu ko guda ba.

 

Lamarin da ya sanya Gusau ya samu ƙuri’u 39, Jimilla da hakan ya sa shugaban gudanar da zaben Mai Shari’a Malik ya ayyana shi a matsayin sabon shugaban hukumar ta NFF, zaɓaɓɓe.

 

A ɓangare ɗaya kuma shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba Felix Anyasi Agu , ya zama mataimakin shugaba na daya , bayan samun ƙuri’u 23.

 

Sai kuma abokin karawar sa Sanata Obinna Ogba , da ya samu ƙuri’u 8 kacal a zaben da ya gudana.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories