Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar jin dadin alhazai ta baiwa maniyyata mako guda su cika kudadensu

Hukumar jin dadin alhazai ta baiwa maniyyata mako guda su cika kudadensu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Jin dadin alhazai ta jihar Kano ta baiwa maniyyatan da suka biya wani bangare na kudaden aikin hajjin bana wa’adin mako guda su cika kudadensu.

Babban sakataren hukumar Alhaji Muhammad Abba Danbatta ne yayi wannan bayanin yayin taron manema Labarai ranar Alhamis.

Ya ce za a rufe karbar kudin daga ranar Juma’a 12 ga Maris din da muke ciki.

Haka kuma ya ce hukumar ba za ta sake bayar da wata dama ba idan maniyyata suka gaza biyan kudaden bayan cikar wa’adin.

Babban sakataren ya kuma bukaci wadanda shekarunsu suka haura 65 da su je hukumar domin karbar kudadensu.

Idan za a iya tunawa dai tuni hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta baiwa jihar Kano adadin kujera 2229.

Sai dai adadin wadanda suka biya kudin ajiya tun a shekarar 2019 sun zarta adadin kujerun Kano.

Wannan ce ta sanya hukumar ke bukatar duk wanda ke bukatar zuwa aikin hajjin a bana da ya gaggauta cika kudinsa kafin cikar wa’adin.

Wannan ne dai zai baiwa hukumar damar baiwa masu son biyan kudin aikin hajjin a bana, idan masu ajiya basu cika ba.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...