Amirul Hajjin bana na Kano kuma Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya bukaci jami’ai da mambobin kwamitocin da ke gudanar da ayyukan kula da maniyyatan Hajjin bana da su kara himma da jajircewa domin tabbatar da nasarar aikin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban tawagar yada labarai ta a Hajjin bana Mustapha Muhammad ya fitar, inda Sarkin ya jaddada muhimmancin sadaukarwa, hadin kai da aiki tare tsakanin dukkan kwamitocin.
Ya ce wajibi ne jami’an su ci gaba da aiki tukuru tare da mayar da hankali wajen cimma manufofin da aka sanya a gaba, yana mai cewa hadin kai da aiki tare su ne ginshikin gudanar da ayyukan alhazai cikin tsari da nasara.
A nasa jawabin, Mataimakin Amirul Hajj kuma Sarkin Karaye, Muhammad Mahraz Karaye, ya ce babban burin shugabannin tawagar shi ne tabbatar da cikakkiyar nasarar aikin hajjin bana, inda ya ce shirye-shiryen Mina da Arafat na daga cikin muhimman matakan da suka zama ginshikin gudanar da aikin Hajji.
Haka kuma, ya umarci kwamitoci da su shirya tare da mika rahotanninsu bayan kammala ayyukan Arafat domin hada cikakken rahoton aikin Hajjin na bana akan lokaci.
A jawaban su daban-daban shugabannin kwamitocin sun tabbatarwa shugabancin Amirul Hajj da cewa za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar aikin hajjin na bana.
