Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci takwarorin sa na jihohin Najeriya da suyi koyi da gwamnatinsa wajen tura masu dakko rahoto na Musamman zuwa ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati domin ƙarfafa aikin gwamnati, bunƙasa ci gaba, da ƙarawa al’umma damar shiga cikin harkokin mulki.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake bude taron Arewa Media Summit 2026, wanda aka gudanar a dakin taro na Coronation dake Gidan Gwamnatin Kano.
Gwamna Abba ya ce gwamnatin sa ta gina kyakkyawar alaƙa da kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin ƙwararru, ciki har da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), domin inganta aikin jarida da tabbatar da isar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ga jama’a yadda ya kamata.
Gwamnan ya bayyana taron a matsayin wanda ya zo a daidai lokacin da ake bukatar sa, inda ya ce yawaitar yaɗuwar labaran ƙarya, da bayanai marasa tushe, da yaɗa bayanan da ke yaudarar jama’a na barazana ga haɗin kan Najeriya da amanar dake tsakanin jama’a ga gwamnati.
A da haka ne gwamnan, ya yi kira ga gwamnatoci, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara haɗa kai domin tunkarar ƙalubalen domin tabbatar da Najeriya a matsayin ƙasa 1 dunƙulalliya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa samar da yanayin da ke baiwa kafafen yaɗa labarai damar gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci tare da ƙarfafa’ yancin faɗar alvarkacin baki ga jama’a wadanda suka dace da ka’idojin dimokuraɗiyya.
