Gwamnatin Kano ta ce tana shirin kafa kotun tafi-da-gidanka domin gaggauta sauraren shari’o’in da suka shafi miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan zamantakewa.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Sanarwar ta ce samar da kotun zai taimaka wajen hanzarta aiwatar da adalci, ƙarfafa bin doka da kuma zama izina ga masu aikata irin waɗannan laifuka.
Sanarwar ta rawaito Gwamna Yusuf na jaddada kudurin gwamnatin sa na kakkabe barazanar da miyagun kwayoyi da suke yi ga al’ummar jihar musamman matasa maza da mata.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa gwamnan na bukatar kwamitin kar ta kwana da gwamnatin sa ta samar kan yaki da miyagun kwayoyin days zage damtse wajen cimma nasarar da aka sanya a gaba.
