Jarumin Kannywood, Ali Rabi’u Ali, ya mayar da martani kan kalaman fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu Rarara da ya ce wajibi ne ga duk masu sana’ar Kannywood su tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shi ba zai amince da hakan ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ali Rabi’u Ali ya ce mutane da dama sun tambaye shi ko kalaman Rarara na nufin dole ne ya bi wannan umarni.
Jarumin ya ce mahaifinsa ne kaɗai yake da ikon yi masa umarni kan irin wannan al’amari, yana mai bayyana cewa biyayya ga iyaye wajibi ce a Musulunci.
Sai dai ya jaddada cewa addinin Musulunci ya kuma koyar da cewa babu biyayya ga wani abin halitta idan hakan zai saɓa wa umarnin Mahalicci.
