Majalisar Masarautar Gaya ta maida Alhaji Ibrahim Sabo Muhammad kan mukaminsa na Dagacin Panda da ke karamar hukumar Albasu a jihar Kano.
Hakan ya kawo ƙarshen dakatarwar masarautar ta yi masa.
Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da Majalisar Masarautar Gaya ta fitar, mai ɗauke da sa hannun Babban Kansila mai kula da harkokin gudanarwa kuma Wamban Gaya, Alhaji Dakta Mansur Ibrahim Gaya.
A cewar takardar, mayar da shi bakin aiki ya fara aiki ne daga ranar Juma’a 15 ga watan Mayun shekarar 2026 bayan amincewar Mai Martaba Sarkin Gaya.
Majalisar ta bayyana fatan cewa Alhaji Ibrahim Sabo Muhammad zai ci gaba da jagorantar al’ummar Panda cikin adalci da riƙon amana.
