Gwamnatin Kano ta gayyato kwararru Inda suka horas da ma’aikatan Hukumar Sufurin Jihar, wato Kano Line, tare da ɗaukar ƙarin ma’aikatan wucin Gadi guda 100 domin ƙarfafa ayyukan hukumar.
Kwamishinan Sufuri na Kano, Barrista Haruna Isa Dederi, ne ya ƙaddamar da taron horaswar, inda ya buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da damar wajen ƙara ilimi da ƙwarewarsu a harkokin sufuri.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na aiwatar da sauye-sauye da gyare-gyaren da za su inganta harkokin sufuri a jihar.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Farfaɗo da Kano Line, Alhaji Sa’idu Abdullahi Shu’aibu, ya ce an shirya taron ne domin sabunta ilimin ma’aikatan kan sabbin ƙalubale da sauye-sauyen da ake samu a harkokin sufuri na zamani.
- Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Abdullahi Shu’aibu cewa, motocin hukumar ta sa ta Kano Line na gab da fara amfani da motocin iskar gas ta CNG a ayyukanta, hakan ce ta Sanya aka shiryawa ma’aikata horaswar domin su fahimci yadda sabon tsarin take.
