Ɗan takarar shugaban ƙasa na jami’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi zargin cewa yawan sace ɗalibai a makarantu ya ƙaru a ƙarƙashin gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu idan aka kwatanta da gwamnatocin da suka gabata.
Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya tuna da sace ɗaliban makarantar Chibok a shekarar 2014.
Peter Obi ya ce sace ɗaliban Chibok ya haifar da martani mai ƙarfi a cikin gida da ƙasashen duniya, wanda ya haddasa gangamin #BringBackOurGirls.
Sai dai ya nuna damuwa cewa, duk da ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai a baya-bayan nan, ba a nuna irin waccan damuwar ba.
A cewarsa, a cikin shekaru takwas na gwamnatin Muhammadu Buhari an samu kusan hare-haren sace ɗalibai 10, yayin da a cikin shekaru uku kacal na gwamnatin Bola Tinubu an riga an samu sama da hare-hare 10 kokuma makamantan haka.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma soki yadda shugabanni ke mayar da hankali kan zabe maimakon magance matsalolin rashin tsaro da talauci.
Ya ce mafitar matsalolin Nijeriya ita ce shugabanci mai nagarta, da riƙon amana da tausayi, tare da kira ga matasa su ci gaba da taka rawa wajen neman sauyi a ƙasar nan.
