Wasu ’yan mata biyar sun yi nasarar gudowa daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram a Karamar Hukumar Gwoza Jihar ta Borno.
Rundunar Sojojin Operation Hadin Kai ta ce ta ceto ’yan matan ne a ranar 4 ga Yuni, yayin da ake ci gaba da sintiri da hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.
Ta bayyana cewa, sojojin bataliya ta 82 sun ceto Aisha Idris mai shekara 13 da Fatima Abubakar mai shekara 11 a kusa da yankin Amuda da ke Karamar Hukumar Gwoza.
Yan matan sun tsare daga hannu yan Boko Haram din ne daga yankin Sahalawa bayan hare-haren bama-bamai da sojoji suka kai, wanda ya tilasta wa ’yan ta’addan barin wuraren da suka mamaye.
Bayanan farko sun nuna cewa, ’yan matan ’yan asalin yankin Pulka ne, kuma an sace su tun shekarar 2025 din data gabata.
Sauran ’yan mata uku kuma sun miƙa kansu ga sojojin rundunar ta 26 ta Task Force Brigade da ke Gwoza bayan sun tsere wa daga tsaunukan Mandara.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da nuna ƙwazo da ƙwarin gwiwa a yaƙin da take yi da ta’addanci.
