Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHajj 2024: NAHCON Ta Yi Jigilar Maniyya Sama Da 10,000

Hajj 2024: NAHCON Ta Yi Jigilar Maniyya Sama Da 10,000

Date:

Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta ce kawo yanzu ta yi jigilar maniyyata 10,675 zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali a bana.

Wannan na kushe cikin wata sanarwa da jamiā€™ar yada labaran hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar ga manema labarai a jiya Talata.

Ta ce jirgin Flynas mallakin Saudiya yayi jigilar maniyyata 4,665 sai kuma Max Air da yayi jigilar 4,479 yayin da Air Peace kuma ya yi jigilar 1,531.

Ta kara da cewa kawo yanzu ba a a samu kin tashin wani jirgi ba, sai dai dan tsaiko da aka samu a jihar Kwara da ya kamata su tashi ranar 20 ga wata aka mayar da shi 21 ga Mayun da muke ciki.

Ta kuma shawarci maniyyatan da su baiwa kansu hakuri lokacin dawowa, su sani hukumar na da tsarin wanda aka fara kaiwa shi za a fara dawowa da shi gida

 

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muʙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muʙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...