Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum biyu bisa zargin cin zarafin jami’an tsaro da kuma hana su gudanar da ayyukansu na bisa doka yayin wani samame a cikin birnin Bauchi.
Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin, waɗanda aka bayyana sunayensu da Friday, wanda ba a gano cikakken sunansa ba, da Yunana Ali, a ranar Asabar, 3 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe tara na safe a kan titin Yelwa da ke Bauchi.
Ya ce jami’an rundunar ‘E’ Division ne suka tsayar da motar da Friday ke tukawa a yayin gudanar da aikin sintiri na yau da kullum ƙarƙashin shirin Operation Velvet, inda suka nemi a nuna musu takardun motar.
Sai dai a cewar kakakin, waɗanda ake zargin sun ƙi bin umarnin jami’an, suka zama masu zafin rai, tare da kai musu hari. Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikinsu ya yayyage kayan aikin wani sufeto na ’yan sanda a yayin rikicin.
Bayan faruwar lamarin, jami’an sun yi nasarar shawo kan waɗanda ake zargin tare da kai su ofishin ‘E’ Division, inda aka fara gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi musu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da abin da ya faru, yana mai bayyana shi a matsayin yunƙurin tauye ikon hukuma da kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaro na tabbatar da zaman lafiya.
Rundunar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da kira ga jama’a da su bi hanyoyin da doka ta tanada wajen shigar da ƙorafe-ƙorafe kan ayyukan ’yan sanda, maimakon ɗaukar doka a hannunsu.
