Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da zuba jari wajen bunƙasa albarkatun ɗan Adam ta hanyar inganta ilimi, koyar da sana’o’i, ƙarfafa matasa da samar da ayyukan yi domin bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa kan yaƙi da sha da safarar miyagun kwayoyi a Kano.
Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali kan baiwa matasa ilimi, inganta ƙwarewarsu ta sana’o’i domin dogaro da kai, da nufin dauke hankalin matasan jihar daga kan tu’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u.
A cewar sa ci gaba da saka hannun gwamnati ta hanyar zuba jari a albarkatun ɗan Adam zai samar da dubban guraben ayyukan yi da damar kasuwanci ga matasa, rage zaman banza, dakile aikata laifuffuka da ƙarfafa tattalin arzikin jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa babu wata ɗorewar ci gaba da za’a samu ba tare da saka jari a rayuwar al’umma ba, tare jaddada cewa gina al’umma mai ilimi, ƙwarewa da ƙarfin tattalin arziki na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa.
