Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila, ya ce amincewar gwamnatin tarayya na kafa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a kano na daga cikin manyan nasarorin da aka samu wajen kawo ci gaba ga jihar da yankin sa.
Sanatan ya bayyana hakan ne lokacin da gwamna Abba Kabir Yusuf yake bayyana tabbatar da samuwar kwalejojin biyu a yankin Kano ta Kudu.
Kawu Sumaila ya ce kafa cibiyoyin zai faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi da harkokin kiwon lafiya, tare da samar da guraben aiki da bunƙasa tattalin arzikin al’umma, musamman a yankin Kano ta Kudu.
Sanatan ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince da ayyukan tallafawa manoma kusan dubu shida a faɗin Kano ta Kudu da injinan ban ruwa da rijiyoyi, tare da ayyukan gina da gyara hanyoyi, gadoji, magudanan ruwa da kuma yaƙi da zaizayar ƙasa.
Kawu Sumaila ya ce an ware kuɗaɗe domin gina hanyar kilomita 30 da za ta haɗa Garko da Kibiya, yana mai jaddada cewa nagartar wakilci ta fi bayyana ne ta hanyar ayyuka da cibiyoyin da wakilan jama’a suka samar domin inganta rayuwar al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sanatan na cewa an mayar da kwalejin koyar da harkokin raya Akarkara daga Rano zuwa ƙaramar hukumar Sumaila, domin samarwa sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Rano damar fara aiki yadda ya kamata.
