Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kashe fiye da naira tiriliyan 3 wajen tallafa wa masu amfani da wutar lantarki tsakanin Yuni 2023 zuwa Disambar 2025.
Gwamnatin ta ce an bayar da tallafin ne domin rage wa ’yan Najeriya radadin ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka samu a cikin wannan lokaci.
Adadin kuɗin da aka kashe kan tallafin wutar lantarkin na cikin fiye da naira tiriliyan 30 da biliyan 64 da gwamnatin tarayya ta ce ya ƙara matsin lamba kan kashe-kashenta tsakanin Yuni 2023 da Disambar 2025.
Wannan bayanin ya sake jawo hankali kan girman kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke kashewa wajen rage wa ’yan Najeriya nauyin kuɗin wutar lantarki, musamman a yayin da farashin kayayyaki da sauran tsadar rayuwa ke ci gaba da ƙaruwa.
Gwamnatin ta ce tallafin na daga cikin matakan da take ɗauka domin rage tasirin sauye-sauyen farashin wutar lantarki ga masu amfani da ita a faɗin ƙasar.
