
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB), Yusuf Kabir, ya gargadi malaman da ke wasa da aikinsu ko nuna sakaci wajen gudanar da ayyukansu da su gyara halayensu, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci duk wani sakaci da zai janyo koma baya ga harkar ilimi a jihar ba.
Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci daraktoci da manyan jami’an SUBEB domin gudanar da ziyarar duba makarantu a yankin Karamar Hukumar Makoda, domin tantance yadda harkokin koyarwa da ilmantarwa ke gudana.
A yayin ziyarar, Malam Yusuf Kabir ya zagaya wasu makarantu inda ya gana da malamai da dalibai tare da duba yadda ake gudanar da darussa da kuma halartar malamai a ajujuwa.
Labarin ɗaukar malamai 3,917 a Kano ba gaskiya bane – SUBEB
Ya yabawa malamai masu jajircewa da sadaukar da kai wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata, yana mai cewa irin wannan kokari na taimakawa wajen bunkasa ilimi da gina kyakkyawar makomar yara.
Haka kuma, ya umarci Sakataren Ilimi na yankin da ya fito da sabbin tsare-tsare da dabarun kara habaka ilimi, musamman ta fuskar kula da halartar malamai, inganta koyarwa da samar da yanayi mai kyau ga dalibai domin samun ingantaccen ilimi.
A wani bangare na karfafa gwiwar malamai, shugaban hukumar ya bayar da umarnin bai wa wasu daga cikin malaman makaranta tallafin bashin sayen abin hawa domin saukaka musu zirga-zirga da kara musu kwarin guiwa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ziyarar na daga cikin kokarin Hukumar SUBEB Kano na tabbatar da ingantaccen ilimi tare da kara sanya ido kan yadda ake gudanar da harkokin ilimi a fadin jihar Kano.
