Jam’iyyar NDC da ƙungiyar Obidient Movement sun mayar da martani ga kalaman tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, kan tikitin takarar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
A wata ganawa da manema labarai da ya yi a ranar Talata, Ganduje ya bayyana cewa haɗakar Obi da Kwankwaso a ƙarƙashin jam’iyyar NDC ba za ta samu nasara a Jihar Kano ba a zaɓen da ke tafe.
Sai dai shugaban ƙungiyar Obidient Movement na ƙasa, Dr. Yunusa Tanko, ya ce goyon bayan da jam’iyyar NDC ke samu daga al’umma shi ne zai kasance ginshiƙin nasararta a zaɓe.
Tanko ya kuma ce Ganduje ba shi da hurumin yin hasashen makomar tikitin Obi da Kwankwaso, tare da yabawa da irin ayyukan ci gaba da shugabannin biyu suka aiwatar a lokacin da suka jagoranci jihohinsu a matsayin gwamnoni.
A nasa ɓangaren, kakakin jam’iyyar NDC, Abdulmumin Abdulsalam, ya ce tasirin siyasar Ganduje a Kano ya ragu, yana mai cewa jam’iyyarsu na da cikakken kwarin gwiwar samun nasara a jihar.
