Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin gyara kurakuran da aka tara a ƙarƙashin gwamnatocin da suka gabata, yana mai neman a ƙara ba ta damar kammala ayyukan da ta fara.
Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, yayin wata addu’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Shugaban ya ce alamun zaman lafiya da ci gaba na ƙara bayyana a ƙasar, yana mai cewa Najeriya na kan hanyar da za ta fita daga matsayin ƙasa mai tasowa.
Ya ƙara da cewa akwai damammaki da dama da Najeriya ta rasa a baya, da kuma wasu waɗanda ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba, yana mai cewa gwamnatin da yake jagoranta na ɗaukar matakan gyara waɗannan kura-kurai.
Manyan jami’an gwamnati ne suka halarci taron addu’ar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; wasu gwamnonin jihohi; ministoci; ’yan Majalisar Tarayya; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da manyan hafsoshin sojojin Najeriya.
