Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sake tunatar da maniyyatan Hajjin 2027 cewa yau ce ranar ƙarshe da aka sanya domin kammala wasu muhimman matakan rajistar aikin Hajjin.
Hukumar ta ce wa’adin da hukumomin Saudiyya suka kayyade ya shafi kammala shigar da bayanan maniyyata da sauran muhimman bayanan da ake buƙata cikin tsarin Hajjin.
NAHCON ta yi gargadin cewa rashin kammala waɗannan matakai cikin wa’adin da aka kayyade na iya shafar guraben Hajjin da aka ware wa maniyyatan Najeriya.
Hukumar ta kuma buƙaci hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta kammala ayyukan da suka rataya a kansu.
Shirye-shiryen Hajjin 2027 sun haɗa da rajistar maniyyata, biyan kuɗaɗen Hajji da kuma shigar da bayanan mahajjata cikin tsarin dijital na Saudiyya.
