Rundunar ƴansandan Jihar Zamfara ta bayyana cewa jami’anta sun kashe sama da ƴan bindiga 30 a wani artabu da suka yi a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Yazid Abubakar, ya fitar, ya ce artabun ya faru ne yayin da ƴan bindigar ke ƙoƙarin kai hari domin yin garkuwa da mutane a yankin.
Rundunar ta ce jami’anta sun dakile harin tare da kashe sama da 30 daga cikin maharan.
A nasa ɓangaren, Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Zamfara, Mustapha Jafaru Kaura, ya yaba wa jami’an tsaron bisa nasarar da suka samu.
Kaura ya bayyana cewa nasarar na ƙara ƙarfafa fatan samun zaman lafiya, tare da nuna ci gaban da ake samu a ƙoƙarin shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar.
