ungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya (MURIC) ta buƙaci a dakatar da jarrabawa a dukkan cibiyoyin Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya, sakamakon zargin hana wasu ɗalibai mata Musulmi masu sanya hijabi shiga zaurukan jarrabawa.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa an tilasta wa wasu ɗalibai cire hijabinsu kafin a ba su damar shiga jarrabawar ƙarshe ta neman zama lauyoyi, wadda aka gudanar ranar Asabar, 31 ga Oktoban 2026.
A cikin wata sanarwa da daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar ranar Lahadi, MURIC ta buƙaci a gudanar da bincike kan lamarin, tana mai cewa matakin ya saɓa wa haƙƙin ƴancin addini da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Ƙungiyar ta kuma yi barazanar gudanar da zanga-zangar lumana a cibiyoyin makarantar koyon aikin lauya da ke faɗin ƙasar, idan ba a biya buƙatunta ba.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya ba ta mayar da martani kan zarge-zargen ba.
