Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya yi barazanar bayyana wasu bayanai da ya ce za su iya tayar da hankali game da Peter Obi da zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
Datti ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Symfoni, inda ya zargi magoya bayan Peter Obi, waɗanda aka fi sani da Obidients, da kai masa hare-haren kalamai a duk lokacin da ya bayyana ra’ayinsa kan tsohon abokin takararsa.
Ya ce har yanzu shi mamba ne mai biyayya ga jam’iyyar Labour Party, amma ba zai amince a hana shi faɗin albarkacin bakinsa ba.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan ya soki matakan da Peter Obi ke ɗauka na shiga haɗakar siyasa ta jam’iyyar ADC.
Wannan matsayi ya jawo suka daga wasu magoya bayan Obi, waɗanda suka zargi Datti da cin amanar tsohon abokin takararsa da kuma yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, aiki.
Sai dai zarge-zargen magoya bayan Obi ba su zama hujjar cewa Datti na yi wa Atiku aiki ba, yayin da shi ma bai bayyana takamaiman bayanan da yake barazanar tonawa ba.
