Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiZamu rufe gidajen mai 30,000 matuƙar gwamnati ta gaza biyan bashin biliyan 200, -IPMAN.

Zamu rufe gidajen mai 30,000 matuƙar gwamnati ta gaza biyan bashin biliyan 200, -IPMAN.

Date:

Kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN), tace za ta rufe gidajen mai 30,000 matukar gwamnatin tarayya ta gaza biyan bashin Naira biliyan 200 da ta ke binta.

Ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar bayan taro da shugaban kungiyar mamallaka rumbunan adana man fetur, Yahaya Alhassan ya fitar a Abuja.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewar, hukumar da ke kula da kasuwancin albarkatun man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) wacce mallakin gwamnatin tarayya ce, ta gaza biyan bashin, wanda ya ci gaba da taruwa tun cikin watan Satumbar 2022.

Hakkokin tura mai wasu kudade ne da gwamnati ke biyan dillalan mai saboda safarar albarkatun man fetur din da aka loda daga rumbunan adana man zuwa jihohin da ke fadin kasar nan.

Latest stories

Related stories