Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ziyarci Maiduguri a ranar Asabar domin jajanta wa Rundunar Sojin Najeriya da gwamnatin Jihar Borno kan hare-haren da aka kai wa sojoji.
An kai hare-haren ne a Benisheikh, Ngamdu da Pulka, inda aƙalla sojoji 18 suka rasu, tare da wasu fararen hula.
Shettima, ya ce ya kai ziyarar ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.
Ya yaba da jajircewar sojojin wajen kare ƙasa, yana mai cewa ba za a manta da irin sadaukarwar da suka yi ba.
A yayin ziyarar, ya gana da manyan hafsoshin soji da jami’an gwamnati da ke kula da ayyukan tsaro a yankin.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa sojoji da iyalan waɗanda abin ya shafa.
