24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiYanzu-Yanzu: Ana gunar da zanga-zangar EndSars a Jihar Lagos

Yanzu-Yanzu: Ana gunar da zanga-zangar EndSars a Jihar Lagos

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Legas sun harba hayaki mai sa hawaye  kan masu zanga-zangar EndSars da ake gudanarwa a halin yanzu domin nuna jimamin shekaru biyu da kisan da su ke zargin an yi wa ‘ƴan uwansu a Kofar Lekki da ke jihar Legas.

Masu zanga-zangar dai na yin tattaki a kofar Lekki a wani bangare na bukukuwan tuna wa da zagayowar ranar, an ce sun yi arangama da ƴan sandan da ke ɗauke da makamai da aka tura domin kwantar da tarzoma.

Folarin Falana, wanda fitataccen jarumi ne da kuma mawakin kasar nan da aka fi sani da Falz ne su ka jagoranci tattakin  da yake gudana a yanzu haka a jihar ta Legas a safiyar nan

A cewar wata sanarwar da aka raba wa manema labara game da jadawalin yadda tattakin zai kasance, jerin gwanon motocin za su bi ta kofar karbar harajin ta Lekki, inda suke dauke da tutocin kasar nan tare da rera taken #EndSARS.

Latest stories