Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCire tallafin Mai:IPMAN ta gargadi Sarki Sunusi da El-Rufa'i

Cire tallafin Mai:IPMAN ta gargadi Sarki Sunusi da El-Rufa’i

Date:

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN, ta ja kunnen tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i da su daina babatun Kiran gwamnatin ta cire tallafi Mai.

 

Kungiyar ta ce, Idan aka yi la’akari da halin da kasar nan ke ciki cire tallafin man fetur baki ɗaya zai kara jawo yan kasa wahala ne kawai musamman talakawa.

 

Kungiyar ta IPMAN ta mayar da martani ne kan kalaman Sanusi a wajen taron tattalin arziki da zuba jari na Kaduna karo na 7.

 

An dai jiyo Sarkin na nuna Jin tausayin shugaban kasar da Zaizo a nan gaba saboda irin kalubalen tattalin arzikin da ke jiran sa, musamman batun tallafin man fetur da kuma biyan basussuka.

 

Shugaban kungiyar IPMAN, reshen Arewa, Alhaji Bashir Danmalam ne ya bayyana hakan yayin da yake zanta wa da manema labarai a Kano ranar Talata.

 

A cewar Danmalam, tsohon gwamnan babban bankin kasa da El-Rufa’i sun dade suna magana kan cire tallafin a duk fagen da suka samu kansu.

 

“Abin da zai faru bayan an janye tallafin iskar gas (desiel), farashin duk wani abu da za ka yi tunani ya tashi a matsayin litar dizal a yanzu ana sayar da shi a kan N850,” in ji Shugaban IPMAN.

 

“Tuni aka fara yin gyare-gyare a fannin mai ta hanyar zartar da dokar PIA da shugabannin kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.

 

“Dole ne a yaba wa mahukuntan kamfanin na NNPC kan yadda suka tsaya tsayin daka wajen ganin an zartar da dokar masana’antar man fetur (PIA) tare da aiwatar da ita ga wasikar.

 

Game da maganar da Sarki Sanusi ya yi a kan yawan man fetur da ake amfani da shi a kasa, Dan mallam ya hore shi da ya zo su kai shi defo-defo domin ya tabbatar da cewa akwai isasshen man fetur kuma ya fahimci cewa shigo wa da shi a ke yi ko ba shigo wa da shi ƙasar nan a ke ba.

 

Ya ƙara da cewa akwai lokacin da IPMAN ta rubuta wa Shugaba Buhari da ya kafa kwamiti, a haɗa da hukumar kididdiga ta ƙasa, NBS domin binciken yawan man fetur da ake amfani da shi a kasa.

 

“Sabo da haka ina kira ga shugabannin nan biyu da su maida hankali kan abubuwan da za su amfani talakawa, maimakon yin maganganu a kan kudurorin da ba na talaka ba ne,” in ji shi

Latest stories

Related stories