Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciFarashin kayayyaki ya karu da kaso 20.77 a Nageriya - NBS

Farashin kayayyaki ya karu da kaso 20.77 a Nageriya – NBS

Date:

Ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayayyaki a cikin kasar  nan yayin da ya kai kashi a 20 a cikin 100,kana ake kara samun karin farashi  kayan abinci da makamashi da kuma faduwar darajar naira.

Wasu alkaluma da Hukumar kididdiga ta kasar nan ta fitar sun nuna cewa an kara samun hauhawar farashin kayayyakin da ya kai kashi 20.77 a watan Satumba daga kashi 20.52 da yake a watan Agusta, wanda ba a taba ganin irin sa ba tun shekarar 2005.

Kayan masarufi su yi tashin gwauron zabi zuwa kaso 23.4, idan aka kwatanta da kashi 23.1 da yake a watan Agusta.

Ana kuma ganin cewa matsin lamba zai iya sanya kwamitin tsare-tsare mai kula da kudi na Babban Bankin kasar nan CBN ya kara yawan bashi da yake ciyowa a karo na hudu a jere a watan Nuwamba.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories