33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiASUU: Malaman jami’o’i ka iya  fuskantar wahala wajen komawa makarantun su

ASUU: Malaman jami’o’i ka iya  fuskantar wahala wajen komawa makarantun su

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Shugaban kungiyar malaman Jami’o’in kasar nan, Farfesa Emmanuel Osodoke, ya bayyana ce mambobin kungiyar za su fuskantar matsaloli wajen komawa jami’o’in su a ranar Litinin saboda rashin kudin mota.

Farfesa Osodoke ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, ta cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels game da jingene yajin aiki da sukayi.

Shugaban na ASUU ya kuma ce lokutan baya malaman Jami’a suna zaune ne a gidajen da aka gina musu a cikin makarantun su, sai dai yanzu lamarin yasha ban-ban inda matsuguni yake musu wahalar samu a cikin makarantun.

‘’A lokacin baya malamai suna samun sauki wajen gudanar aikace-aikacen su na

Ya kuma kara da cewa mallaman ka iya shan wahala wajen tafiya makarantun nasu saboda rashin biyan su albashi na tsawon wattani 8 da suka kwashe suna yajin aiki.

koyarwa sannan suna samun gidajen zama a cikin jami’o’in ba tare da matsala ba sabanin yanzu da gidajen suke nesa da kamarantun su, Ta ya ya za su iya biyan kudin mota zuwa aiki,” in ji Osodoke.

Latest stories