Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ƙwato bindiga da harsasai guda 48 a tashar mota ta Rijiyar Zaki.
wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar.
Sanarwar ta ce, ’yan sandan Dorayi Babba sun je tashar motar ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, bayan samun bayanai daga wani mutum, inda suka gano bindigar da harsasan a cikin wani kunshin kaya.
Rundunar ta ce, wanda ake zargi da hannu a lamarin ya bayyana cewa ya sayi bindigar da harsasan ne daga wata jiha domin tura su ga wani mutum a wata jihar.
Sanarwar ta ce, ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a wasu ayyukan da Rundunar ta gudanar, an kama mutane biyar bisa zargin fashi da makami a garin Jajaye da ke Ƙaramar Hukumar Rogo, sannan an ƙwato wata saniya da rago da aka sace a Gaya.
