Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta sanar da samun nasarar dakile wani yunkurin kai hari bayan jami’anta sun gano tare da lalata wani bam da aka kera a gida da ake zargin wasu ‘yan bindiga ne suka dasa a yankin Kunchin Kalgo da ke Karamar Hukumar Tsafe.
A wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar a jiya, ya bayyana cewa jami’an Sashen Yaki da Muggan Laifuka tare da hadin gwiwar Sashen Kwararru Masu Lalata Abubuwan Fashewa sun samu nasarar gano tare da lalata bam din cikin kwarewa ba tare da an samu asarar rai ko dukiya ba.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:15 na yammacin ranar Asabar, bayan rundunar ta samu sahihan bayanan sirri daga al’umma game da wani abu mai hadari da aka binne a gefen hanya.
Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun dasa bam din ne domin haddasa mummunar barna da asarar rayuka ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A.M. Bello, ya bukaci jama’a su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da gaggauta sanar da hukumomin tsaro duk wani abu da suka gani da zai iya zama barazana ga zaman lafiya da tsaro.
