Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniYadda 'almajirai' ke biyan naira 20 ko 50 don samun wajen kwana...

Yadda ‘almajirai’ ke biyan naira 20 ko 50 don samun wajen kwana a Kano

Date:

Mahukunta a jihar Kano sun ce sun gano wani gida da ke karɓar N20 zuwa N50 domin bai wa ƙananan yara masu gararamba da mabarata makwanci.

Rahotanni sun ce almajiran, wadanda ciki har da mata da kananan yara, har bashi sukan ci don su biya kudin da za a ba su makwanci a wannan gida.

A cewarsu yanayin gidan da ake bai wa almajiran makwanci ya yi kama da gidan kallon kwallo.

Hukumar da gwamnatin jihar Kano ta dora wa alhakin kamen almajirai ce ta kai samame wannan gida wanda a yanzu aka rufe shi.

Bayanai sun nuna cewa yawancin yaran da aka kama a gidan ba almajirai ba ne, wasunsu sun gudo ne daga gaban iyayensu.

Daya daga cikin irin wadannan yara da suka gudo daga gaban iyayensu suka zo bara Kano, ya shaida wa BBC cewa dole ce ta sa ya zo wannan gida yake kwana.

“Kishiyar mahaifiyarmu ce take duka na, ga shi ba ta ba ni abinci, akwai ranar da na ta aike ni tsautsayi ya sa na yar mata da naira 50, a ranar bayan duka har sai da ta yanke ni da reza”.

Abinci kuwa sai ta ga dama ta ke ba ni, wani lokacin ma sai wanda ‘ya’yanta suka ci suka rage take ba ni, wani lokacin kuma kanzo nake ci, in ji yaron.

Yaron ya ce mahaifiyarsa ba ta gidan tana can jihar Jigawa tana aure, su kuma suna Kano, yana mai cewa da a ce mahaifiyarsa da mahaifinsa suna tare babu abin da zai kawo shi kwana wannan gida.

“A gaskiya ni kai na ba na jin dadin halin da na tsinci kaina, to amma ba yadda zan yi, ga shi ko makaranta ba na zuwa, yanzu sai dai na je na yi gwangwan na samu kudi na ci abinci sannan na biya kudin wajen kwana,” a cewar yaron.

Shehi Bakhari Mika’il, shi ne shugaban hukumar kula da kamen almajiran, ya shaida y ace da suka je kamen almajiran sun kama yara sun kai 84, 68 daga cikinsu ba makarantar allo suka zo Kano ba.

Ya ce, wasu azaba ce ta kishiyar uwa ta kawo su gidan, wasu kuwa anan aka yi cikinsu har aka haifesu a wajen.

Shugaban hukumar ya ce,”A yanzu mun kamo iyayen wasu daga cikin yaran, za a kai su kotu, wadanda kuma ke da wata matsala ta gida mun kira hukumar kare hakkin dan adam ta kasa domin tabi musu hakkinsu”.

Yawon bara tsakanin yara da manya a jihohin arewacin Najeriya wata babbar matsalace data gagari jihohin da ke yankin tsawon shekaru.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...