Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaCovid-19: Firaminstan Burtaniya na fuskantar barazanar tsigewa daga kan mulki

Covid-19: Firaminstan Burtaniya na fuskantar barazanar tsigewa daga kan mulki

Date:

Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson, na fuskantar barazanar saukewa daga mukaminsa bayan an fara binciken shi bisa zargin karya dokokin kariyar COVID-19 a lokacin da cutar take ganiyarta a kasar.

Ana tuhumar Mista Boris Johnson da gudanar da taruka ba bisa ka’ida ba a gidansa da ke birnin Landan, inda a wajen tarukan aka rika yi wa dokokin kariyar COVID-19 hawan-kawara.

Rahotanni sun nuna daga hawansa mukamin Fira Ministan Birtaniya zuwa yanzu, an zarge shi da shirya taro akalla sau 17 a gidansa, kuma dukkaninsu babu wanda aka bi matakan kariyar COVID-19.

Jama’a da dama a Birtaniya sun shiga sukar Fira Ministan da rashin kyautawa a abin da ya aikata.

Ko a watan Disambar 2021, sai da aka yi ta caccakar Mista Johnson kan halartar wani taron casu da ya yi, wanda hakan ya fusata yawancin mutanen kasar, amma daga bisani ya fito ya nemi afuwarsu.

Tuni jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike a kansa, kuma akwai yiwuwar tilasta masa yin murabus daga mukaminsa na Fira Minista da zarar an same shi da laifi.

Latest stories

Related stories