Saurari premier Radio
37.8 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaYadda maganin ‘Akurkura’ ya shanye min barin jiki

Yadda maganin ‘Akurkura’ ya shanye min barin jiki

Date:

Wani dan kasuwa a nan Kano Muhammad Ibrahim ya bayyana yadda maganin Karin kuzari na ‘Akurkura’ ya haddasa masa shanyewar barin jiki.

PREMIER RADIO ta ruwaito maganin da masu sana’ar maganin gargajiya ke sayarwa na da karfin gaske da ke sanyawa mutum ya fita daga hayyacin sa lokacin da ya kurkura.

Galibin masu yin amfani da wannan magani sunce duk da cewa maganin na kara musu kuzari, ya kuma kawar da dukkan ciwon da ke jiki amma yana kusan hallaka mutum lokacin da yake kuskurawa.

Muhammad Ibrahim ya ce abokin kasuwancinsa ne ya kawo masa maganin, da nufi magance matsalar sanyi da kasalar da ke damunsa.

“Ranar Juma’a na je kasuwa wani abokina ya bani maganin a kurkura, su dai naga suna kurkurawa ko da yaushe, amma ni sau daya na kurkura, kawai sai na fara jin kai na najuyawa, nan da nan na fara amai.

“Nayi ta amai ba kakkautawa, nan da nan jikina ya kama karkarwa, lamarin da ya sa na koma gida sai dai kafin wani lokaci jikina ya tsanata.

“Kashe gari aka kai ni asibitin Murtala, bayan likita ya dubani ne kuma aka maiyar da ni asibitin koyarwa na Aminu Kano.

“A nan likita ya yimin gwaji saboda hannuna na dama da kafata tuni sun daina aiki, a she na samu shanyewar barin jiki.” Muhammad ya bayyana.

Sai dai Muhammad ya ce yana da nasanin kurkura maganin, inda ya kirayi jama’a da su kaucewa amfani da irin wadanan magunguna na gargajiya haka kawai.

Pharmacists Najib Bello da ke zaman shugaban kungiyar masu nazarin magani ta kasa ya nuna takaicinsa kan wannan al’amari.

Ya ce babban abinda ke jawo irin wannan shi ne yadda jama’a ke amfani da maganin gargajiya saki ba kaidi, ba tare da la’akari da halin da za su shigaba.

“An dade ana sayar da maganin gargajiya a kasar nan, amma galibinsu ba a la’akari da yadda ya kamata a yi amfani da su sai kawai a dirkawa mutum.

“Jama’a basa yin tambaya kafin yin amfani da maganin gargajya, kuma basusan irin sinadarin da aka yi amfani da shi wajen hada maganin ba.

An dai sha samu irin hadari ga mutane da yawa da suke kurkura wannan magani a nan Kano da ma wajen Kano.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...