Kungiyar kare hakkin Dan Adam ta IHRC- ta bukaci gwamnati ta gaggauta duba matsalolin da suka shafi tsarin fanshon tsofaffin jami’an ’yan sanda, tare da ƙarfafa tsarin kula da lafiyarsu.
A karshen watan satumban da ya gabata ne tsofaffin jami’an yan sanda suka gudanar da zanga zanga a jihar Ogun in da suka bukaci shugaba Tinubu ya dubi hakkokin su na fansho domin rage musu wahalar rayuwa.
Kungiyar tace Zanga-zangar lumana da tsofaffin jami’an ’yan sanda suka gudanar kan matsalolin da suka shafi fansho da jin daɗinsu na buƙatar kulawa ta musamman daga Gwamnatin Tarayya.
Daraktan kungiyar a Najeriya Amb Abdullahi Bakoji Adamu a wata sanarwa da ya fitar, yace su ma tsofaffin Yan sanda ’yan ƙasa ne da suka sadaukar da shekaru masu yawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma ƙasa, Don haka, ya kamata a saurari koke-kokensuna fansho
