Dangote ya ware kyautar Naira dubu 500,000 ga masu ba da bayanan sirri kan safarar haramtattun kaya da motocinsa.
Kamfanin Dangote ya ƙaddamar da wani shiri na karɓar bayanan sirri daga jama’a domin yaƙi da safarar haramtattun kaya ta hanyar amfani da manyan motocinsa.
Kamfanin ya ce duk wanda ya bayar da sahihan bayanan da suka kai ga kama masu laifi ko kwato kayayyakin da ake safara ba bisa ƙa’ida ba, za a ba shi kyautar Naira 500,000.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a Legas, ya ce wannan shiri na daga cikin matakan da yake ɗauka domin kare ingancin harkokin jigilar kayansa tare da dakile ayyukan wasu mutane da ke amfani da motocin Dangote wajen safarar kayayyaki ko mutane ba tare da izini ba.
Kamfanin ya buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani zargi na amfani da motocin Dangote wajen safarar kayayyakin da ba a amince da su ba, yana mai jaddada cewa motocin kamfanoninsa an ware su ne domin jigilar kayayyakinsa.
Dangote ya kuma bayyana cewa ya bai wa jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda, ikon kama duk wani direba da aka samu yana amfani da motocin kamfanin wajen kasuwanci ba tare da izini ba.
