Wasu yan bindiga da ake zargin masu alaƙa da Boko Haram sun kai hari kan wasu al’ummomi a jihar Adamawa State, inda suka kashe aƙalla mutane 29 tare da jikkata wasu da dama.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne a ƙaramar hukumar Gombi, musamman a ƙauyen Sabon-Gari da ke gundumar Guyaku da kuma yankunan da ke kusa da su ciki har da Telabala.
Mazauna yankin sun ce maharan sun kai harin ne da yammacin ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:00, a lokacin da jama’a da dama suka taru domin kallon wasan ƙwallon ƙafa a wata makarantar firamare.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigar sun iso kan babura, suna harbi ba kakkautawa, abin da ya jefa yan wasa da masu kallo cikin firgici yayin da suke tserewa domin tsira.
Wani mazaunin yankin, Bala, ya ce ya ƙirga gawarwaki 29, yana mai cewa akwai wasu da dama da har yanzu ba a san inda suke ba.
An kuma ruwaito cewa maharan sun ƙone wata coci, tare da lalata kayan kiɗa da kujerun roba. Haka kuma, an ƙone aƙalla babura 42 mallakin yan wasa da masu kallo a filin wasan.
Wannan hari ya sa gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya katse wasu muhimman ayyukansa inda ya kai ziyara yankunan da abin ya shafa domin jajanta wa al’umma tare da duba halin da ake ciki.
A yayin ziyarar, gwamnan ya tabbatar da cewa kimanin mutane 29 ne suka rasa rayukansu, yana mai bayyana harin a matsayin abin takaici, raɗaɗi da kuma wanda ba za a amince da shi ba.
Ya kuma nuna damuwa cewa harin ya zo ne mako guda kacal bayan makamancin wannan hari da ya faru a Mayo Ladde a ƙaramar hukumar Hong.
