Saurari premier Radio
34.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniWesley Fofana ya kamala komawa Chelsea daga Leicester City

Wesley Fofana ya kamala komawa Chelsea daga Leicester City

Date:

Ahmad Hamisu Gwale

 

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta kammala siyan dan wasa Wesley Fofana daga Leicester City a kan kudi fam Miliyan 70.

 

Fofana ya amince da sanya hannu a kwantaragin shekara shida a kungiyar da ke birnin London.

Wesley Fofana da mamallakin Chelsea
Wesley Fofana da mamallakin Chelsea

Mai shekara 21, ya zama cikin ‘yan wasan baya da ake saran Thomas Tuchel zai yi amfani da su a tawagar ta Stamford Bridge.

 

A baya dai an yita samun koma baya wajen kammala ciki tsakanin kungiyoyi biyun, kafin daga bisani a wannan rana a kammala cinikin.

 

Kawo yanzu dan wasan kasar Faransa ‘yan kasa da shekara 2, ya zama na shida da Thomas Tuchel ya dauka bayan Gabriel Slonina, Carney Chukwuemeka, Kalidou Koulibaly, Raheem Sterling da kuma Marc Cucurella.

Latest stories

Related stories

Zargin shigar magoya baya fili ya sanya anci tarar Pillars Miliyan Daya

Mahukuntan shirya gasar Firimiyar Najeriya, sunci tarar kungiyar kwallon...