An sake rantsar da Shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, a matsayin sabbin Shugabannin da zasu ja ragamar jam’iyyar na tsawon shekaru 4 masu zuwa.
Zaben wanda aka gudanar da shi a dakin taro na Murtala Square dake jihar Kaduna, an gudanar da shi ne a tsarin masalaha wato consensus, inda aka sahalewar Shugabannin dake Jan ragamar jam’iyyar su dora daga inda suka tsaya.
Shugabannin da aka rantsarwar sun hadar da Muhammad Garba, a matsayin Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma Shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, sai Isa Sadiq Sakataren shiyyar, da Barrister Bashir Hussaini mashawarci a fannin shari’a, sai Musa mai lafiya Sakataren yada labarai, da Abdulhamid Umar Shugaban matasa, sai Dahiru Gambo a matsayin wakilin masu bukata ta musamman tare da Hajiya Hadiza Alhaji Shugabar mata, sai kuma Salisu Uba Tsafe a matsayin matakin Sakatare.
Da yake jawabi a wajen taron, gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa karkashin Jagorancin jam’iyyar su ta APC jihar Kaduna ta samu gagarumin ci gaba a fannin tsaro, tare da yin kira ga Shugabannin da aka rantsar da su ci gaba da yin jagorancin cikin adalci.
Shi ma a nasa bangaren sabon shugaban jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya ya sha alwashin ci gaba da daukar matakan da zasu kara wanzar da nasarar jam’iyyar ta APC a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.
