Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWani zaman sulhu da akayi tsakanin ministan kwadago simon lalong da kungiyoyin...

Wani zaman sulhu da akayi tsakanin ministan kwadago simon lalong da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a jiya Litinin, ya tashi ba tare da cimma wata matasaya ba.

Date:

Wani zaman sulhu da akayi tsakanin ministan kwadago simon lalong da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a jiya Litinin, ya tashi ba tare da cimma wata matasaya ba.
Rahotannin sun ce ministan ya kasa bayar da gamsassun bayanai kan dalilan da kungiyoyin suka bayar na tafiya yajin aikin sai baba ta gani mako mai zuwa.
Da yake karin haske ministan kwadago simon lalong ya bayyana kwarin gwiwar samun maslaha duk da gaza biyan bukatun da kungiyoyin suka bijiro dasu a zaman nasu.
Amma y ace ya fahimci irin halin da ma’aikatan kasar nan ke ciki, kuma da sannu gwamnati zata share masu hawaye.
A nasa jawabin shugaban kugiyar kwadago ta kasa NLC Joe Ajaero ya nuna bacin ransa kan yadda gwamnati ke aiwatar da rabon tallafin rage radadin cire tallafin mai, inda yace ba alkawari daya da gwamnati ta iya cikawa har kawo yanu duk kuwa da yajin aikin gargadi na kawanaki biyu da kungiyar ta gabatar.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...