Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBayanai na nuna cewar babban bankin kasar CBN ya fara aiwatar da...

Bayanai na nuna cewar babban bankin kasar CBN ya fara aiwatar da matakin karbo rancen da ya baiwa wasu ‘yan kasar nan domin saukaka musu radadin kuncin tattalin arzikin da barkewar annobar Korona ta haddasa a sassan duniya.

Date:

Bayanai na nuna cewar babban bankin kasar CBN ya fara aiwatar da matakin karbo rancen da ya baiwa wasu ‘yan kasar nan domin saukaka musu radadin kuncin tattalin arzikin da barkewar annobar Korona ta haddasa a sassan duniya.
Bankin CBN dai ya bayar da tallafin rancen ne a tun shekarar 2020.
Bayanai sun ce tuni bankin na CBN ya fara cire kudaden da yake bin wasu da ya bai wa rancen daga asusunsu, sai dai wasu na korafi akan tsarin da ake bi wajen karbar kudaden, inda a maimakon a rika janye musu kudaden a hankali, sai a rika zaftare jimillar adadin kudaden tallafin da suka amfana da shi a lokaci guda, abinda suka ce yana matukar jefa su a cikin kuncin gurguncewar gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Wani batu kuma da a yanzu yake daukar hankali shi ne alwashin da gwamnatin tarayya ta yi na kammala karbo tallafin rancen kudaden da ta bai wa dubun dubatar manoman, a karkashin shirin ‘Anchor Borrower’ da aka fara a shekarar 2015, domin inganta ayyukan noma.

A jiya Litinin ne dai wa’adin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kayyade na tabbatar da cewa an karbo bashin noman daga wadanda suka amfana ya cika.

Latest stories

Related stories