Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWani matashi ya nemi iyayen budurwar sa da su biya shi babur...

Wani matashi ya nemi iyayen budurwar sa da su biya shi babur dinsa da aka sace masa.

Date:

Wani matashi ya nemi iyayen budurwar sa da su biyashi babur dinsa mai kafa biyu da aka sace masa yana tsaka da yin zance da budurwar tasa a falon gidan su.

Lamarin ya faru ne a unguwar Tukuntawa a daren ranar Alhamis.

Matashin mai suna Muhammad Sani, ya ce yana cikin cin shinkafa dafa duka sai budurwar tashi tashigo tana tambayar sa inda babur din nasa yake.

Nanfa ya tsame hannunsa daga kwanon abinci tare da rugawa kofar gida a guje.

Matsalar tsaro:Malisar wakilai ta yi barazanar tafiya yajin aiki

Ya ce da farko ya zata da wasa take amma daga bisani ya fahimci cewa dagaske ne an sace baburin nasa wanda ya ajiye a kofar gidan su budurwar tasa.

Yace babur din nasa kirar roba roba ne kuma bai dade da siyansa ba.

Haka zalika bayan da ya kafe tare da kin tafiya ‘iyayen budurwa tasa suka nemi da ya dawo ranar Juma’a don sanin abinda za a ayi.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories